Daga Umar Faruk
Shugaban karamar hukumar Yauri, Honarabul Abubakar Shuaibu Kauran Yauri ya shirya liyafar cin abincin ga kansilolinsa da mataimakinsa. Wannan karimcin don ya nuna jin dadinsu kan yadda suka yi fice a yayin wani taron bitar sanin makamar aiki na gudanar da Mulki a matakin kananan hukumomin a jihar Kebbi da gwamnatin jihar ta shirya ga dukkanin kansiloli na kananan hukumomi 21.
Taron wanda aka gudanar a otal din Dankane dake jihar Sakkwato, an yi shi ne domin baiwa kansiloli sanin ayyukansu da tsarin mulki. Shugaba karamar hukumar Yauri kuma Kauran Yauri ya umurci duk kansilolin da su halarci liyafar cin abincin daren na yau Lahadi a gidansa, kuma kowa da kowa ya halarci liyafar, ciki har da mataimakin shugaban Karamar Hukumar ta Yauri a daren Lahadi yau.
Tags
Hausa news