Shugaban Kasar Nijar Ya kaddamar Da Taron kwanaki Uku Na 'Yan Jaridun Afirka Ta Yamma Masu Yada Labaru Da Harshen Hausa


Shugaban Kasar  Nijar Ya kaddamar Da Taron kwanaki Uku Na  'Yan Jaridun Afirka Ta Yamma Masu Yada Labaru Da  Harshen Hausa

Daga Abdullahi Faruk Birnin Kebbi

Shugaban kasar Nijar, Birgediya Janar Abdoulrahmane Tchiani, ya kaddamar da wani taro na kwanaki uku ga 'yan jaridun Afirka ta Yamma masu yada labaran harshen Hausa. Taron wanda ya samu halartar ‘yan jarida daga kasashe 11 na da nufin inganta amfani da harshen Hausa a matsayin harshen da za a rika amfani da shi a  hukumance a yammacin Afirka.

Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine shi ne ya wakilci shugaban kasar tare da jaddada muhimmancin amfani da harshen Hausa wajen inganta al'adu, zaman lafiya, jituwa, hadin gwiwa, tsaro, da bunkasa tattalin arziki. Ya bukaci mahalarta taron da su fito da hanyoyin da za su inganta hadin gwiwa da kwanciyar hankali a yankin kasashen.

Taron zai mayar da hankali ne kan "Haɓaka zaman lafiya, kwanciyar hankali, da dangantakar aiki tare a tsakanin ƙasashen yammacin Afirka: Ra'ayin Jarida." Ana sa ran 'yan jarida za su ba da shawarwari  kan yadda za a inganta hadin gwiwa da kwanciyar hankali a yankin.

Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da Hajiya Mariama Sarkin Azabin, shugabar kungiyar ‘yan jaridun yammacin Afirka masu amfani da harshen Hausa daga Jamhuriyar Nijar, Hajiya Naja’atu Muhammad da Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya daga kasar Nijeriya da dai sauransu.

Makasudin taron zai yi duba ne kan Haɓaka haɗin gwiwar yanki da haɗin gwiwar tattalin arziki, Ƙarfafa tattaunawa da diflomasiyya. Haka kuma Haɓaka hanyoyin dakile rikici da hanyoyin warware rikici. Kazalika akwai bukatar Ƙarfafa cibiyoyin yanki da haɓaka iya aiki da samar da mu'amala tsakanin mutane da al'adu.

Bugu da kari, samar da hadin gwiwar tsaro da dimokuradiyya a wadanda Karshen da dai sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post