Daga: Umar Faruk Birnin Kebbi
Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma fitaccen ɗan siyasa daga Arewa, Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya mayar da martani ga wata sanarwa da ake dangantawa da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, inda ya ce duk wanda ya rike mukamin gwamnati cikin shekaru ashirin da suka wuce ya kamata ya nemi afuwa daga Arewacin Najeriya.
Sanata Na’Allah ya bayyana cewa bai ga wani dalili da zai sa ya nemi afuwa ba, domin ya yi wa Najeriya da Arewa hidima da gaskiya da rikon amana. Ya ce, ya taba yin aiki tare da Sanata Uba Sani a majalisar dattawa, kuma babu wani mataki da ya dauka da ya cutar da yankin Arewa.
Sanata Na’Allah ya bukaci Gwamna Uba Sani da ya bayyana su waye ya kamata su nemi afuwa da kuma kan wane dalili.
Ya kuma jaddada cewa, muddin ba a daina barin son zuciya wajen zaben shugabanni ba, Arewa za ta ci gaba da fuskantar koma baya.
Tags
Hausa