Daga: Umar Faruk Birnin Kebbl
A wani gagarumin yunkuri na shawo kan matsalar tsaro da kuma munanan ayyuka da ke faruwa a masarautar Yauri, Shugaban karamar hukumar Yauri, Abubakar Shuaibu Kauran Yauri ya kira taron gaggawa da shugabannin kungiyoyin ‘yan banga. Babban makasudin taron dai shi ne warware Matsalar jagororin da ta dade ana rigingimun da suka kawo cikas ga kokarin yaki da barazanar tsaro a Karamar Hukumar.
A yayin taron, Kauran Yauri, ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin kungiyoyin ‘yan banga, inda ya jaddada cewa, dole ne a aje yin bangaranci domin samun ci gaba ta Fuskar Samar da tsaro a Karamar Hukumar Mulki ta Yauri. Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta sayo kayan aiki don rabawa ga dukkanin kungiyoyin ‘yan banga a fadin kananan hukumomin 21, amma zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin na da matukar muhimmanci wajen amfani da wadannan kayan don in babu hadin kai don yin aiki guda, idan ba a samu hakan ba, akwai Matsalar don gwamnatin ba zata yi aiki dabamgaranci ba.

Kauran Yauri ya kuma yi tsokaci kan illar rashin hadin kai, inda ya bada misali da yadda gwamnati ta sanya kayayyakin aikin jama’a da aka lalata wasu kuma an sace sun hada da cibiyar sadarwa ta koyon na'ura mai kwakwaluwa ta garin Yauri da cibiyar Samar da ruwan sha da aka gyara a kwanakin baya . Ya kuma bada tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda suka aikata laifin lalatawa da sacewa gaban kuliya domin fuskantar fushin doka idan aka samu nasarar cafke su, inji shi.
Shugaban ya yabawa kokarin Gwamna Nasir Idris na tallafawa kungiyoyin ’yan banga, musamman ma kudirin sayo sabbin motocin sintiri ga daukacin kananan hukumomi 21. Sai dai ya jaddada cewa wannan tallafin zai yi tasiri ne kawai idan kungiyoyin sun hada Kansu waje guda da kuma aiki cikin kwanciyar hankali.
Hakazalika, Shugaban ya bukaci hadin kai tsakanin su, Haka kuma Kauran Yauri ya kara da cewa ina da burin karfafa aikin tsaro da tabbatar da yin amfani da kayan gwamnati yadda ya kamata wajen yakar kalubalen tsaro a Masarautar Yauri. Wannan mataki yana da matukar muhimmanci, saboda taka tsantsan na iya nuna wasu bangarori na gazawar gwamnati, kuma rashin tsawatar wa ga bangarorin na iya haifar da illa fiye da alheri.
A Nijeriya, taka-tsantsan ya bayyana a matsayin mayar da martani ga gazawar shugabanci, musamman a yankunan da ke da yawan al'adu da rashin zaman lafiya a hukumomi. Ingantacciyar haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin 'yan banga, don haka, yana da mahimmanci don magance matsalolin tsaro da haɓaka zaman lafiyar al'umma.

Tags
Hausa news