Sanata Garba Mai Doki Ya Kaddamar Da Shirin Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 45 Ga Daliban A Mazubun Kebbi Ta Kudu
By Umar Faruk Birnin Kebbi
Sanata Garba Musa Maidoki, mai wakiltar mazabun Kebbi ta Kudu, ya kaddamar da shirin “Students and Youth Educational Empowerment Programme”, idan bayar da kyautar N35,000 ga dalibai 1,291 daga mazabarsa dake karatu a jami’o’i daban-daban a fadin Nojeriya.
Shirin ya shafi daliban da suka Karatu a Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Zuru, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Aliero, Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake jihar Sakkwato, Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Jami’ar Jos a jihar filato, da Jami’ar Bayero dake a jihar Kano.
A cewar Farfesa Ahmed Umar Sanda, shugaban kwamitin tantancewa da biyan kudaden, ya ce dalibai masu na matakin 100 ne daga jami’o’in da aka kayyade, aka zaba ta hanyar tantance bayanansu da kuma takardunsu na asali.
Wadanda suka amfana sun hada da Dalibai 291 daga FUA Zuru, Dalibai 141 daga UDU Sokoto, Dalibai 292 daga FUBK, Dalibai 514 daga KSUSTA, Dalibai 14 daga BUK, Dalibai 11 daga Uni Jos, Dalibai 28 daga ABU Zaria.
A wajen bikin kaddamar da bikin bayar da tallafin ya gudana ne a cikin Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta koyon aikin Gona ta Zuru, Farfesa Sanda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kyautar tallafin karatun bisa gaskiya, sannan ya shawarci iyaye da masu kula da su da su tabbatar da yin amfani da kudaden yadda ya kamata.
Mrs. Chinyere Ezem, mai lura da ayyukan daga cibiyar samar da kayayyaki ta kasa, Abuja, ta jaddada mahimmancin dalibai su inganta kan basirarsu da kuma mai da hankali kan karatun su. Ta kuma bayyana bukatar yin amfani da kudaden tallafin yadda ya kamata.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin Hauwa Abdulkarim da Sirajo Salisu sun nuna godiya ga Sanata Maidoki tare da yi masa addu’ar samun nasara.
Tags
Hausa