Kwamitin Bayar Da Tallafin Karatu Na Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805 A Kebbi


Kwamitin Bayar Da Tallafin Karatu Na  Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805  A Kebbi 


Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi

Kwamitin bayar da tallafin karatu na Sanata Garba Musa Maidoki mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu, ya biya jimillar dalibai sama da  805 domin samun tallafin karatu.

Biyan kudaden ya hada da dalibai 291 daga Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Zuru (FUAZ) da Kuma dalibai 514 daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke  Aliero (KSUSTA).

Haka kuma kwamitin ya tono   ɗalibi da  KSUSTA ɗaya saboda rashin sahihan bayanai ga  takardu da zasu nuna shedar cewa asulin wanda aka gano daga Karamar Hukumar Mulki ta Yauri ya fito ko ta fito amma bayanai na nuna cewa dalibin ko dalibar daga Karamar Hukumar Mulki ta Birnin Kebbi ne. 

Bisa hakan ne kwamitin Suka sallami wanda aka gano daga rashin basu wa kudin tallafin karatun. Domin ka'idar shi ne sai wanda ya gwadi shedar zama dan kananan Hukumomin da suka kunshin Mazubun Kebbi ta kudu, ko daga masarautar Yauri ko Zuru.

Daliban da kwamitin ya tantance sahihincin takardun su sun karbi Naira 35,000 kowanne bayan an Kammala  tantance su.

Shugaban kwamitin Farfesa Umar Ahmad Sanda ya bayyana jin dadinsa da aikin, inda ya yabawa ‘yan kwamitin bisa kwazon da suka yi.

Farfesa ya bayyana cewa takardun da ake bukata sun hada da takardar zama dan asalin karamar hukuma, katin shaidar zama dan kasa, ba da izinin shiga jami’a, da katin shaidar zama ɗalibi a  jami’a.

Dalibin da aka hana ya yi ikirarin cewa daga  karamar hukumar Yauri ya fito ko ta fito amma  takardun da aka gabatar sun nuna cewa mallakar karamar hukumar Birnin Kebbi ce.

Shugaban kwamitin ya bukaci dalibai da su yi watsi da kansu idan ba su da takaddun da ake bukata, yana mai gargadin cewa  bincike zai gano duk wanda bai ke da bayyanan Karya ko takardun maras sahihanci.

Ya kuma yaba da goyon bayan da ‘yan kwamitin, shugabannin jami’a, da kuma Sanata Maidoki suka samu a bisa jajircewarsa na karfafa wa matasa musamman masu Karatu a jami'o'in kasar nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post