Daga: Sokoto
Shugaban hukumar zabe ta jihar Sakkwato Aliyu Sulaiman a ranar Litinin ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben dukkanin kananan hukumomi 23 da aka gudanar a ranar Asabar.
Haka ma APC ta lashe dukkanin kujerun kansiloli a zaben wanda jam'iyyu 15 suka shiga, sai dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kauracewa shiga zaben.
Jim kadan da bayyana sakamakon, hukumar zaben ta jihar ta baiwa zababbun shugabannin kananan hukumomi takardar shaidar lashe zabe.
Tags
Hausa news