Shugaban Kamfanin MTech Ya Taya Musulmai Murnar Bikin Mauludi A Kebbi


Shugaban Kamfanin MTech Ya Taya Musulmai Murnar  Bikin Mauludi A Kebbi 

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi 

Manajan Daraktan Mtech Universal Concept, Arc. Munir Musa Jega, ya aike da sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi a kan bikin Mauludi na Maulidin Annabi Muhammad (SAW).


A wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, Injiniya Manir Jega ya taya Gwamna Nasir Idris da al’ummar Jihar Kebbi murnar wannan gagarumin biki na addini.


Haka kuma ya bukaci al’ummar musulmi da su dage wajen ibadarsu, su yi koyi da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, tare da inganta soyayyar ’yan’uwa, tausayi da kyautata wa makwanci da mabiya sauran addinai.


Ya kuma yi kira da a ba da hadin kai, biyayya, da addu’o’i ga shugabanni a kowane mataki, da kuma samar da zaman lafiya da tsaro ta hanyar kare rayukkan da dukiyoyin 'yan kasar Nijeriya.

Kazalika, Injiniya Manir Musa Mai ya ja hankalin mazauna jihar Kebbi da su bada hadin kai ga kokarin gwamnatin jihar na inganta rayuwa da bunkasar tattalin arziki domin Kara samun ci gaba mai amfani a jiharmu ta Kebbi.

"Ina yi wa daukacin musulmi barka da zagayowar ranar  bikin Idi-Maulud," in ji Injiniya Jega.



Post a Comment

Previous Post Next Post