Sanata Maidoki Ya Shirya Rarraba Taki Ga Kananan Hukumomi 7 Dake Kebbi Ta Kudu


Sanata Maidoki Ya Shirya Rarraba Taki Ga Kananan Hukumomi 7 Dake Kebbi Ta Kudu

Daga Umar Faruk 

Sanata Garba Musa Maidoki mai wakiltar mazabun Kebbi ta kudu zai raba takin zamani ga mazabun sa dake fadin kananan hukumomi bakwai. Shirin na da nufin bunkasa noma, da kara samar da abinci, da kuma rage wahalhalu da yunwa da Jama'a ke faskanta.


Manufofin Rarraba taki shi ne Haɓaka ayyukan noma, haɓaka samar da abinci, biyan buƙatun samar da abinci mai yawa  a cikin al'ummarmu . Saukake Wahalhalu da Yunwa da Inganta jin daɗin jama'a gaba ɗaya

Ana sa ran rabon takin  zai amfanar da Jama'a musamman manoma, wanda zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin 'yan kasa . Sai dai lokacin rabon kayayyakin ya shafi sadaukarwar Sanata Maidoki da kansa, domin a ranar Asabar din nan ne aka shirya daurin auren ‘yarsa.

Kokarin da Sanata Maidoki ya yi ya nuna cewa ya jajirce wajen tallafawa al’ummar mazabun sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post