Jihar Kebbi Ta Nada Sabon Mukadashin Shugaban Ma'aikata




Daga Umar Faruk Birnin Kebbi 

Hajiya A’isha Usman ta zama  shugabar Mukadashiyar ma’aikatan gwamnati a jihar Kebbi, inda ta gaji Safiyanu Garba Bena wanda ya yi ritaya bayan ya cika shekaru 60 da haihuwa, an gudanar da bikin mika ragamar mulki a ofishin majalisar zartarwa da ke Birnin Kebbi.


Shugaban ma’aikata mai barin gado, Safiyanu Garba Bena, ya bayyana jin dadinsa ga Gwamna Nasir Idris bisa damar da ya ba shi na yin aiki batare da wata katsalanda ba , ya kuma godewa ma’aikatan gwamnati da masu aikin yada labarai bisa goyon bayan da suka ba shi na tsawon shekaru uku. Ya kuma yi wa magajinsa fatan alheri don ciyar da ma’aikatan gwamnati a mataki na gaba.


Hajiya A’isha Usman, tsohuwar sakatariyar din-din-din a  Ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren  tattalin arziki a jihar, ta yi alkawarin dorawa kan abin da magabacinta ya bari da kuma cimma burin da aka sa gaba.


 Ta amince da amincewar da aka yi mata tare da neman hadin kai da goyon baya daga ma’aikatan gwamnati da kuma kafafen yada labarai a cikin da wajen jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post