Daga Umar Faruk
Daliban Jami’ar Usmanu Dan fodiyo da ke jihar Sakkwato da dai sauransu sun yabawa Sanata Garba Musa Maidoki bisa shirin bayar da tallafin karatu na ilimi a kyauta. Shirin ya amfana da dalibai da ke a mataki farko wata agji Daya daga jami'o'i bakwai a fadin kasar, ciki har da: Usmanu Danfodiyo University Sokoto, Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi Aliero, Jami'ar koyon Aikin Gona ta Gwamnatin Tarayya da ke Zuru.
Sauran sun hada da Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, Ahmadu Bello University Zaria, Bayero University Kano da kuma Jami'ar Jos a jihar filato.
Kowane dalibi ya karbar Naira 35,000. Wadanda suka ci gajiyar tallafin Hauwa Umar da Habibu Musa Isgogo da sauransu sun bayyana godiyarsu, inda suka ce tallafin zai rage musu matsalolin Karatu da kuma tallafa wa iyayensu.
Shugaban kwamitin Shirin ba da tallafin na Sanata Maidoki, Farfesa Umar Ahmad Sanda, ya bayyana tsarin tantancewa da biyan kudi, tare da tabbatar da gaskiya da adalci. Sama da dalibai 100 ne aka biya a Jami’ar Usmanu Dan fodiyo da ke jihar Sakkwato, tare da biyan wasu kudade a wasu jami’o’in.
Haka kuma shugaban kwamitin ya kara da cewa Shirin ya nuna yadda Sanata Garba Musa Maidoki ke da himma wajen samar da ilimi da ci gaban matasa mazabun da ya ke wakilta a Majalisar dattawan Nijeriya.